Majalisar Dinkin Duniya tace ta samu rahotanni da suka bayyana cewa dakarun gwamnatin Syria a Aleppo sun kashe a kalla farar hula 82 a unguwanni hudu, kuma kungiyar agaji ta Red Cross tayi kashedin dubbai a gabashin Aleppo ba su da wajen da zasu gudu su tsira.
Shugabannin yammacin Afirka sun isa Gambia domin lallashin Shugaba Yahya Jammeh wanda baya son ya sauka daga mulki bayan shan kaye a zabe.
Wata Kungiyar Kasar Sweden Zata Gina Mazauni A Maiduguri Don Taimakawa 'Yan Gudun Hijira, Disamba 12, 2016
Yawan mutanen da suka mutu sanadiyar tawayyen bama bamai a babban birnin Istanbul ya kai 44, inda 36 yan sanda ne.
Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta aiyyanna cewa akalla mutane 27 ne suka mutu kana wasu 30 suka samu rauni bayan rugujewar wata coci akan masu ibada a kudancin jihar.
'Yan Boko Haram sun kai hari a Maiduguri, Jihar Borno
A cikin shirin namu na yau, zamu leka Najeriya inda aka fara horar da 'yan banga domin cigaba da wanzar da zaman lafiya a duk fädin kasar.
Nana Akufo-Addo Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Ghana
‘Yan sanda 6 sun halaka kana wasu 3 suka ji rauni bayan da wani bam da aka dasa a gefen hanya ya tashi a kusa da shingen bincike jami’an tsaro a birnin Alkahira.
Wasu kafafan yada labaran Ghana sun ruwaito cewa shugaban ‘yan adawa Nana Akufo -Addo ya lashe zaben shugaban kasar.
Jami’ai sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.5 a ma’auni, wadda ta faru a lardin Aceh (acheh) na kasar Indonesia ya kai 105.
A kwanan nan kasar Mali ta yi bukin tunawa da nakasassu a karo na farko a kasar, wanda ake kira Handifestival da Turanci.
Hira tare da Farfesa a fannin Ilimin Ma'adinan kasa na Jami'ar Maradi Malam Ali Moumouni a wani taro da aka gudanar a babban birnin Washington, DC. Disamba 02, 2016
Taron Adu'o'i Da Sojoji Suka Gudanar A Maiduguri, Najeriya. Disamba 07, 2016
Zaben Shugaban Kasar Ghana 2016
An fara gudanar da zabe a Ghana, inda Shugaba John Mahama ke kokarin a sake zabenshi a wa’adi na biyu kuma na karshe.
Shugaba Mugabe ya bukaci a kai zuciya nesa yayin da gwamnatinsa ke kokarin shawo kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar, inda a ke kuma zargin ana amfani da sababi wajen murkushe 'yan tawaye.
Daruruwan malaman makarantun boko ne suka gudanar da wannan jerin gwanon, wanda ya tashi daga dandalin da ake kira Place Toumo zuwa Dandalin fahintar juna dake gaban zauren Majalisar Dokokin Nijar. Malaman dai na neman gwamnatin Nijar ta biya masu wasu bukatunsu.
An karawa tsohon ministan cikin gida Bernard Cazaneuve matsayin zuwa Fira-minista don maye gurbin Manuel Valls wanda ke takarar neman shugabancin kasa.
Domin Kari