Majalisar Dinkin Duniya tace ta samu rahotanni da suka bayyana cewa dakarun gwamnatin Syria a Aleppo sun kashe a kalla farar hula 82 a unguwanni hudu, kuma kungiyar agaji ta Red Cross tayi kashedin dubbai a gabashin Aleppo ba su da wajen da zasu gudu su tsira.