Daruruwan malaman makarantun boko ne suka gudanar da wannan jerin gwanon, wanda ya tashi daga dandalin da ake kira Place Toumo zuwa Dandalin fahintar juna dake gaban zauren Majalisar Dokokin Nijar. Malaman dai na neman gwamnatin Nijar ta biya masu wasu bukatunsu.