Bayan da shugaban yayi ganawa akan habbaka sha’anin noma tsakanin Saudiya da Najeriya, da kuma duba hanyoyin da za a bi domin inganta farashi na Man Fetur.
Mallam Garba Shehu Kakakin shugaban Buhari, yayi karin haske kan sauran ganawar da shugaba Buhari yayi domin samun hanyoyin da za a inganta sha’ani na cinikayya da zamantakewa da kuma karfafa gwiwar ‘yan Najeriya akan fafutar da gwamnatin keyi wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Kakakin, yace za a yi muhimman taro baya ga wadanda akayi na ‘yan kasuwa da masu zuba hannun jari, ana fatan ranar Alhamis idan shugaban yayi Umara ya sauke, zai tattauna da bankin Islama da kungiyar kasashen musulmai wanda zasu kawo masa dauki, wadannan sune manyan tattaunawa da zai yi kuma ana fata cikin tattaunawar za a ji irin gudunmawar da zasu bayar don bunkasa tattalin arziki da farfado da ruywar mutanen Najeriya.
Domin karin bayani.