Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci wata tawagar manya manyan jami’an Gwamnatin Najeriya da Gwamnoni wasu jihohin Najeriya domin yin ziyarar kwanaki hudu a kasar Saudiya.
Shugaban zai gana da takwaransa na Saudiya domin tattauna sha’anin da ya shafi albarkatun Noma da ma’adinai da kuma duba hanyoyin da za’a bin domin inganta farashin Man fetur wanda ya kawo cikas ga tattalin arzikin wasu kasashe dake kungiyar kasashe masu arzikin Mai ta duniya wato OPEC.
Shugaba Buhari ya gana da hukumomin Saudiya domin nemo hanyoyin da Saudiya zata taimaka wajen saka jari a Najeriya a fannonin Noma da Ma’adinai.
Malam Garba Shehu kakakin shugaba Muhammadu Buhari, yace ‘yan kasuwar kasar ta Saudiya sun amince cewa zasu saka jari a Najeriya.
Yana mai cewa bayan amincewar tasu akwai tattaunawar da zai biyo baya akwai kuma shirin da Najeriya keyi domin ta karbi bakunci masu zuba jarin.