Wakilai daban daban daga kasashen Afirka, dama Duniya ke hallartar bikin baje koli kayayyaki sadarwar zamani.
Masana sunyi fashin baki akan hanyoyin inganta harkokin sadarwar zamani ta yarda za’a kaucewa shiga hurumin wasu da basu ci ba basu sha ba walau al’umar ne ko Gwamnati.
Sai dai masana bakinsu yazo daya wajen yin Allah wadarai da matakan da wasu Gwamnatoci na kasashen duniya ko kuma hukumomin tsaro ke dauka na ganin an dakile amfani da kafofin sadarwar zamani.
Wata ‘yar Najeriya da kasar Amurka Ngozi Otita, da itama ta hallarci taron tace tana ganin akwai bukatar sakarwa al’uma mara domin gudanar da harkokinsu ta kafofin sadarwar zamani idan aka ce za’a dauke wani mataki na takurawa na hana al’uma amfani da wannan kafa toh ko shakka babu wannan yana nufin takurawa tare da tauye hakkin da bil-Adama ke dashi.
Shi dai wanna biki na makon kafofin sadarwar zamani ana gudanar da shine a kasashe goma sha biyu a fadin duniya kuma birnin Lagos na daya daga cikin biranan da ake gudanar da wanna biki kuma birnin Lagos ne daya kachal da ake gudanar dashi a nahiyar Afirka Najeriya dai na daya daga cikin kasashen duniya da ake amfani da kafofin sadarwar zamani masamman ma dai Facebook.