Sojojin Faransa uku ne suka mutu cikin makon jiya,sakamakon hadarin da jirgin sojan Faransa mai saukar ungulu yayi a Libya, wanda yasa faransa ta kasance kasar yammacin duniya ta farko da ta fito fili ta tabbatar da cewa, ta girke wasu sojojinta na musamman domin su taimakawa bangarorin da suke yaki da masu tsatstsauran ra'ayi a kasar.
An hakikance cewa sojojin Amurka da Britaniya suna Libya tun wajajejn karshen bara-sojojin Amurka sun girke kansu a Benghazi da Misrata. Amma babu daya daga cikin kasashen da suka fito a hukumance suka amince cewa suna da sojoji a Libya.
Zanga zanga da aka yi a karshen mako, masu ra'ayin addini ne suka shirya shi-ciki harda babban malamin kasar Sheikh Sadek Al-Ghariani, nan da nan zanga-zangar ta zama kiraye kiraye masu karfi cewa tilas Faransa da wasu kasashen ketare su janye sojojinsu daga kasar, har sua yi barazanar zasu maye gwamnatin hadin kan kasar da wata sabuwa.