Mai magana da yawun Machar James Gadet Dak, yace zabar Taban Deng a matsayin mataimakin shugaban kasa na ‘daya ka iya tayar da zaune tsaye na babu gaira babu gaira babu dalili a kasar.
Yunkurin maye gurbin Machar dai ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki biyun da aka baiwa Machar na ya dawo babban birnin Juba. Shugaba Kiir ya gayyaci Machar wanda yake shugaban jam’iyyar adawa ta People’s Liberation Movement, domin su tattauna don samar da masalaha kan rikicin da ya barke tsakanin bangarorin biyu, inda ya yi sanadiyar rasa akalla rayukan mutane 300.
Mai magana da yawun Machar Dak, ya ce nada Taban Deng ba ya bisa ‘ka’ida saboda an kore shi daga kan mukaminsa. Haka kuma yarjejeniyar ta bayyana cewa idan mataimakin shugaban kasa na ‘daya ba zai iya gudanar da aikinsa ba, ya na da hurumin zabar wanda zai iya rike masa mukaminsa, a cewar Dak.