Mawallafa da masu zane-zane da wasan kwaikwayo da mawaka, da ma malamai daga fadin duniya ne ke halarta wannan taro mai muhimmanci na Hargeisa Internation Book Fair da ba sami yayatuwa ba.
A wannan bikin na 9 na yanzu, ya nuna shekaru 9 kenan ana yinsa duk shekara, kasashen 12 ne suka halarta wadannan kasashe kuwa sune Nigeria, Jamus, Birtaniya, Ghana, Italiya, Faransa da kuma Afirka ta Kudu.
Yakin basasar Somalia da shugaban mulkin kama karya Mohamed Siad Barre ne sanadiyyar daidaita cibiyoyin tarihin kasar a shekarun 1980.
Wanda hakan ya dakile matasa da kirkire kirkiren basirar su ballke su nunawa duniya. inji Ayan Mohamoud na cibiyar al’adu ta Kayd.