Daruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar a babban birnin tarayya Abuja, don nuna rashin jin dadinsu kan yadda tsadar rayuwa ke addabar talaka.
Bayan da suka fito daga gidan shugaban kasa, shugaban kungiyar kwadago na Najeriya, Comrade Ayuba Wabba, ya yi jawabi inda ya ce, sun gabatar da bukatunsu ga mukaddashin shugaban kasa, inda suka tuna masa da cewa wannan shine karo na biyu da suke gunadar da zanga –zanga.
Kungiyar ta kwadago ta shirya zanga zangar domin neman kyakkyawan shugabanci da neman ayi yaki da cin hanci na gaskiya a Najeriya.
Ya ci gaba da cewa babu wata alaka a halin yanzu tsakanin Abuja da sauran jihohi, musamman in ana batun albashi ko kudin fanshon tsofaffin ma’aikata.
Bayan haka kuma shugaban kwadagon ya ce mataimakin shugaban Najeriya, ya gaya musu za a duba wadannan batutuwan, amma duk da haka za su ci gaba da gwagwarmayarsu har sai haka ta cimma ruwa.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina daga Abuja.