Kananan hukumomin Rafi da Shiroro da Sarkin Pawa da duk suka yi iyaka da jihar Kaduna ke fama da matsalar 'yanbingan da suka addabesu da kai hare-hare, da kashe mutane da yiwa mata fyade tare da kwashe dabbobi da dukiyoyi.
Yanzu akwai daruruwan jama'a da suka tsere daga muhallansu domin kaucewa 'yanbindigan.
Gwamnatin jihar ta Neja tace ta gamsu da yadda 'yanbangan ke bada gudummawa wajen aikin samarda tsaro a yankin. Dalili ke nan da gwamnati ta dauki matakin taimaka masu.
Jibril Baba Ndaci sakataren yada labaran gwamnan jihar Neja yace sun yadda da 'yanbangan saboda sun fi jami'an tsaro sanin kauyukansu kuma sun san kowa da kowa a yankin. Yace idan wani ya shiga kowane kauyen da ba'a sanshi ba to duk inda ya kutsa kai sun sani. Ababen hawan da aka basu zasu taimaka masu su shiga lungu lungu domin su zakulo bata gari.
A fadar gwamnan jihar aka mikawa shugaban karamar hukumar Rafi Gambo Tanko Kagara baburan, shi kuma ya kaiwa 'yanbangan.
Malam Gambo yace baburan ne suka fi anfani domin wuraren da ake shiga mota bata iya zuwa sai babura.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.