Kamar yadda shugaban hukumar Alhaji Abdu Joro ya shaida ranar Asabar din nan mai zuwa idan Allah ya yadda za'a gudanar da zaben a duk kananan hukumomin jihar.
Yayinda yake yiwa manema labarai jawabi Alhaji Abdu yace jam'iyyu bakawai ne suka yi rajista kuma dukansu ne zasu shiga takarar.
Wuraren dake fuskantar matsalar tsaro mutanen karamar hukumar zasu taru ne a hedkwatar ita wannan hukumarsu su kada kuri'unsu.
A kan kin shiga zabe da jam'iyyar PDP tayi Alhaji Abdu yace kamata yayi a tambayi shugabannin jam'iyyar dalilin da ya sa basu shiga ba. Akan zargin da ita PDP ta keyi cewa ba'a shirya sosai ba, shugaban hukumar zaben yace tunda basu shiga ba basu da hujja domin sai sun shiga zasu san ko ba'a shirya sosai ba.
Bisa ga alamu daga furucin shugabannin sauran jam'iyyun baicin PDP sun gamsu da shirin da hukumar zaben tayi.
Jam'iyyar PDP ta ki shiga zaben saboda wai Nera dubu dari biyu ne kowane dan takarar kujerar kansilo zai biya. A nasu ganin kudin yayi yawa. Ita PDP kawai zata biya Nera miliyan arba'in da bakwai da dubu dari bakwai idan har zata shiga. A ganinsu kudin yayi yawa.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.