Mukaddashin babban daraktan hukumar tsaron farin kaya ta DSS Mr. Matthew Seiyefa a taronsa da manema labarai bayan ya kama sabon aikinsa ya jaddada cewa a tsarinsa zaman lafiya da tsaron Nigeria ne farko da zai sa gabansa yanzu.
Ya ce zasu yi iya kokarinsu wajen kare jama'a tare da gudanar da ayyukansu cikin tsarin da dokar kasa ta tanada. Baicin hakan zasu karfafa kokari wajen tattara bayanan sirri tare da tantance su domin tsare Nigeria. A cewarsa suna cikin tsarin dimokradiya ne kuma ayyukansu zasu bi tsarin da ya dace da dimokradiya.
Bugu da kari, daraktan ya yi alkawarin sake duba tsarin da aka bi a baya,inda hukumar ke tsare mutane ba bisa ka'ida ba.
Masana irinsu Dr Kole Shettima, na maraba da matakin da mukaddashin ya ke shirin dauka. Ya ce maganar Mr. Seiyefa ta farantawa mutane rai, saboda an san cewa akwai mutane da ake tsare dasu da ba'a san inda suke ba, wasu ma ba'a san ko suna da rai ba. Ya yi misali da wani dan jarida da aka tsare sai bayan shekaru biyu aka sako shi, bayan da iyalansa suka dauka baya da rai. Ya ce akwai mutane da yawa da aka kama da ba'a san da labarinsu ba. Ya kamata a duba, duk wanda yake da laifi a kaishi kotu. Wanda kuma bashi da laifi a sake shi, a nemi gafararsa kana a biyashi diya.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum