Jami’in labarun ofishin mukaddashin shugaban Najeriya Laolu Akande, shine ya baiyana haka da nuna Sieyefa zai rike wannan mukami har daukar mataki na gaba.
Sieyefa dai wanda dan asalin jihar Bayelsa ne a kudu maso kudancin Najeriya, shine mataimakin babban daraktan hukumar a sashen aiyuka.
Magoya bayan gwamnatin Buhari irin matashi da ya tattaki daga Lagos zuwa Abuja a ‘kafa don murnar lashe zaben 2015, Sulaiman Hashim ya ce kusanci baya hana shugaba Buhari yin hukunci, kuma hakan ya nuna ba maganar 'yan mowa da bora a gwamnatin.
Baya ga batun rufe Majalisa da ya jawo kwabe Lawal Daura, maganar daukar matakin da ya sabawa na shugaba Buhari kamar takardar hana tantance mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, na ratsowa a ra'ayoyin jama'ar Najeriya.
Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Nuhu Ribado na cewa Magu zai yi galaba.
Za a jira a ga matakan da hukumar EFCC da rundunar 'yan sanda da ke tsare da Lawal Daura za su dauka in an cika sa'a 48 na ka'idar rike wanda a ke tuhuma.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum