Tsohon shugaban hukumar tsaron farin kaya DSS, Lawal Daura da gwamnati ta kora daga bakin aiki ranar talata, yanzu na ofishin yana hanun 'yan sanda na musamman a Abuja, inda zai ci gaba da zama har sai an san matakin da za'a dauka akansa nan gaba.
Tuni ofishin mukaddashin shugaban Nigeria Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce ba da yawun ofishin shugaban kasa ba ne jami'an DSS rufe da fuska tare da sanya bakaken kaya, suka yiwa majalisar dokokin kasar kawanya. Ofishin ya sha alwashin zakulo duk wadanda suka haddasa lamarin domin a hukunta su.
Haka kuma wata majiya mai tushe ta ce jami'an hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa, wato, EFCC sun banzama gidan Lawal Daura, domin gudanar da bincike.
Matakan da Lawal Daura ya dauka na tura wasika zuwa majalisar dattawa na cikin dalilan da suka hana majalisar tantance Ibrahim Magu ya zama shugaban EFCC. Duk lokacin da Magu ya samu yin magana akan batun ya kan ce shi bai damu ba.
Ibrahim Magu yace shi gaskiya ya sa gaba. Babu munafunci. Babu zalunci. Aiki ne da aka basu su keyi. Ya ce shi bai damu ba domin Allah ne yake kare mutum, shi ne kuma yake karban ran mutum.
'Yan siyasa na ci gaba da mayar da martani akan kawanyar da aka yiwa majalisar dokokin. Masani akan lamuran majalisa Alhaji Sa'adu Hassan, ya ce jami'an sun saba doka saboda Lawal Daura da hukumarsa basu da hurumin killace majalisa su hana wakilai da ma'aikata shiga. Ya ce abun da aka yi Lawal Daura shine ya dace dashi.
Dan kwamitin amintattu na kungiyar ta zarcen Buhari Isa Tafida Mafindi, ya ce matakin da gwamnatin Buhari ta dauka ba abun mamaki ba ne. Ya na cewa duk wanda yake tunanin shi ne mutumin Buhari ya kwana da shiri domin ba za'a dade ba da zai yi da na sani da ban yi tunanen "ni mutumin Buhari ba ne". Ya ce Buhari mutum ne da ya zo ya tsaftace Nigeria. Abun da kuma zai yi ke nan. Babu sata, babu mulkin kama karya, kuma babu sani babu sabo.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum