Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakin Korar Lawal Daura Da Mataimakin Shugaban Nigeria Ya Dauka Kare Dimokradiya Ne


Mataimakin Shugaban Nigeria Farfesa Yemi Osibanjo
Mataimakin Shugaban Nigeria Farfesa Yemi Osibanjo

‘Yan Nigeria na ganin matakin da mataimakin shugaban Nigeria ya dauka na korar shugaban hukumar DSS, kare mutuncin dimokradiya ne, kuma ya nuwa cewa babu wanda zai yi mata karan tsaye ya kwana lafiya

Duk da cewa yawancin ‘yan Nigeria sun amince da matakin korar Lawal Daura daga mukaminsa na shugabancin DSS saboda mamaye majalisar dokokin kasa da jami’ansa suka yi, wasu na ganin cewa da walaki goro a cikin miya.

Malam Zailani Bappa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi na ganin cewa salon da Shugaba Buhari ya dauka na barin kowa ya yi yadda yake so, ya sa aka samu Baraka. Yace da Shugaba Muhammad Buhari ya yi anfani da karfin gwamnati da kuma karfin kudi kamar yadda aka saba yi, da an zauna lafiya. Shugabannin majalisun biyu duk daga jam’iyyar PDP suka fito, wannan ne tushen matsalar da aka shiga yanzu. Ya kara da cewa haka Dimokradiya ta gada amma a hankali za’a fahimmci inda aka sa gaba.

Sai dai Malam Yusuf Abdullahi na Kwalajin Kimiya da Fasaha cewa ya yi auren da aka kulla tsakanin wadanda suka fice daga PDP suka shiga APC tun farko bai yi ba. Ya ce ana wasa ne da hankalin ‘yan Nigeria. Akidojinsu sun banbanta. Yana ganin kowa ya gaji da abun dake faruwa kodayake bai dace akai jami’an tsaro a majalisa ba saboda a lokacin da jami’an suka je ‘yan PDP ne suke ciki. Su kuwa ‘yan APC suna wani wuri daban suna tasu harkar saboda haka ana neman a yi wasa ne da hankalin ‘yan Nigeria.idan ba’a yi hankali ba kiru na iya jan bau, wato allura na iya tono garma. Yace kadan da kadan abu ke farawa har ya kai idan ba’a yi zato ba.

A nashi tsokacin, shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kirista Ambassador Aminu Garba Sidi y ace matakin da mataimakin shugaban Nigeria Farfesa Osinbajo ya dauka, kare martabar Dimokradiya ne. Yace Dimokradiya ta bada walwalar a shiga majalisa ba tsangwama. Mataimakin shugaban ya kare Dimokradiya ya kuma nunawa wadanda suke ganin suna iya yi mata karan tsaye, su kwana lafiya. Yanzu sun san basu da wannan dama.

A saurari rahoton Abdulwahab Muhammad

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG