Tarukan neman kuria’ar delegate da masu neman tikitin takarar shugaban kasa karkashin inuwar Jam’iyyar hamayya ta PDP da kuma gangamin da hadiman shugaba Muhammadu Buhari keyi a jihohi domin jaddada goyon baya na daga cikin manyan batutuwan da ke daukar hankali a fagen siyasar Najeriya.
Ko a ranar Asabar din nan, sai da guda cikin mukarraban shugaba Muhammadu Buhari a Kano, Janar Lawal Jafaru Isa, ya yi gangamin hadin kan magoya bayan shugaban, inda har-ma ya nanata cewa, Kanawa masoyan Buhari ne kuma shugaban ya yi musu tanadi na musamman.
Hakan na zuwa ne, a dai dai lokacin da manyan sabuwar APC irin su tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso da shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki, ke ci gaba da tsare-tsaren fita daga jam’iyyar ta APC mai mulki, duk da lallashin su da shugabancin jam’iyyar keyi.
A daya bangaren kuma, masu neman takarar shugabancin Najeriya a PDP na kara ‘kaimi wajen neman kuri’ar Delegates, domin tunkarar babban taron jam’iyyar na fidda gwani wadda zai wakana a cikin watan gobe na Agusta.
A rannar Asabar din nan ce shi-ma Alhaji Atiku Abubakar ya kaddamar da ta sa takarar a karkashin lemar ta PDP a garin Yolan jihar Adamawa.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum