Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Jinkirin Tafiyar Da Shari’u Na Haddasa Take ‘Yancin Bil Adama


 Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai.

Kungiyoyin fafutikar ‘yanci bil’adama a Najeriya sunce jinkirin tafiyar shari’u a kotuna na daga cikin kalubalen da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukan su.

Sai dai masana harkokin doka na ganin lokaci yayi da manyan alkalan kasar za su rinka amfani da damar da suke da ita wajen yanke hukuncin shari’u akan lokaci domin kauce yanayin take hakkin dan Adam.

Batun take hakkin bil’adama na ci gaba da zama ruwan dare a Najeriya a matakai daban-daban, duk kuwa da karuwar alkaluman kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ake samu a kasar.

Sai dai kungiyoyin na kokawa kan irin kalubalen da suke fuskanta wajen bibiyar hakkin masu rauni. Alhaji Bello Gadon Kaya, shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta human rights foundation of Nigeria. Ya yi kira ga alkalai da cewa su rika saka ido da tabbatar da an kammala duk shari’ar da aka gabatar garesu ba tare da bata lokaci ba.

Batun ‘yancin bil’adama na cikin al’amuran da suka mamaye ajandar taron kungiyar lauyoyi musulmi ta Najeriya daya gudana a jihar Kano.

Barrister Ibrahim Yakubu Umar tsohon kwamishinan shari’a na jihar Bauchi ne ya ce taron ya zaburar da manyan alkalai ta wannan fuska.

Tuni dai kungiyoyin ketare irin su Amnesty International suka rinka wallafa rahotanni kan zargin jami’an tsaron Najeriya da take hakkin bil’adama.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG