Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Raba Auren Diyar Ganduje


Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, ta yanke hukuncin a ranar Alhamis na raba auren shekara 16 tsakanin Asiya Ganduje da Inuwa Uba.

Asiya diyar gwamnan Jihar Kano ce, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Abdullahi Halliru, ya ce an raba auren ne ta hanyar Khul’i.

Halliru ya umarci wacce ta shigar da karar da ta mayar da Naira dubu N50,000 da wanda ake kara ya biya a matsayin sadaki.

Sharuddan da wanda ake kara a baya ya gabatar a gaban kotu ya kamata su kasance bisa Sunnar Musulunci a kan Khul’i.

Khul’i na nufin a mayarwa da miji sadakin sa, to bai kamata sharadi ya shafi mata ba, musamman wajen fitar da dukiyarta.

Asiya, ta bakin lauyanta, Ibrahim Aliyu-Nassarawa ya dage kan a mayar da sadakin da ya bawa amarya domin a raba auren.

Tun da farko, lauyan Inuwa, Umar I. Umar ya bayyana cewa batun ya wuce biyan Naira dubu N50,000 na sadaki.

“Wanda ake kara yana da ‘ya’ya hudu tare da mai kara, amma duk kokarin sulhunta su yaci tura,” in ji Umar.

A cikin sharudan sa, Inuwa ya roki Asiya ta mayar masa da takardunsa na gidaje da motoc, i kuma ta sarayar da hakkinta a kamfaninsu na shinkafa da suke hadaka.

Lauyan Inuwa ya kara da cewa za su yi nazarin hukuncin da kotu ta yanke tare da wanda ake kara domin su duba irin mataki na gaba da za su dauka.

XS
SM
MD
LG