Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Nemi Goyon Bayan Masarautar Kano A Zabe Mai Zuwa

‘Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Nemi Goyon Bayan Masautar Kano A Zabe Mai Zuwa
‘Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Nemi Goyon Bayan Masautar Kano A Zabe Mai Zuwa

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasar a zaben bana na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya fara gudanar da taron gangaminsa na neman kuri’a a Kano.

KANO, NIGERIA - Tun da daren jiya Laraba ne, dan takarar ya isa Kano tare da tawagarsa, inda a wayewar garin yau ya bude wata Kwalejin haddar Alqur’ani Mai Girman a garin Gudunwawa na yankin karamar hukumar Gezawa a jihar ta Kano.
‘Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Nemi Goyon Bayan Masautar Kano A Zabe Mai Zuwa
‘Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Nemi Goyon Bayan Masautar Kano A Zabe Mai Zuwa

Kwalejin, wadda sanatan Kano ta tsakiya a majailisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau ya gina, a wani bangare na ayyukan raya mazabu da ‘yan majalisar dokoki a Najeriya ke yi, nada girman azuzuwa da zasu dauki yawan dalibai dari biyar a lokaci guda.

Kazalika kwalejin, wadda za ta kunshi maza da mata dalibai, nada dakunan kwana da filin motsa jiki da kuma gidajen malamai.

‘Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Nemi Goyon Bayan Masautar Kano A Zabe Mai Zuwa
‘Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Nemi Goyon Bayan Masautar Kano A Zabe Mai Zuwa

Bayan bude kwalejin, dan takarar na PDP ya wuce zuwa fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, inda ya nemi tabarriki da kuma samun goyon bayan masarautar Kano domin samun nasara a zabe, yana mai nanata kudirorinsa na hada kan ‘yan kasa da tabbatar da tsaro da kuma farfado da tattalin arziki.

A jawabinsa, mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi fatan alkahiri ga dan takarar tare da tunasar da shi bukatar dake akwai ta kyautata wa al’umma muddin aka sami nasara a zabe.

‘Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Nemi Goyon Bayan Masautar Kano A Zabe Mai Zuwa
‘Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Nemi Goyon Bayan Masautar Kano A Zabe Mai Zuwa

Bayan barin sa fadar Kano, Alhaji Atiku Abubakar ya wuce zuwa filin wasan kwallon kafa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano, inda zai gabatar da jawabi ga dinbin magoya baya.

XS
SM
MD
LG