Shugaban tawagar ya bayyanawa Muryar Amurka dalilinsu na zuwa Najeriya a daidai lokacin da ake tababan ko Yahya Jammeh zai mika mulki cikin ruwan sanyi.
Ahmed Fate shugaban jam'iyyar da ta lashe zabe a Gambia yace suna Abuja ne a hukumance domin marawa shugabannin kasashen Yammacin Afirka baya bisa ga hobasan da su keyi na ganin Yahya Jammeh ya mika mulki wata mai zuwa.
Dama can shugabannin sun ziyarci shi Yahya Jammeh inda suka tattauna dashi akan takaddamar da ta kunno kai. Ahmed Fate yace bayan ziyarar tasu sun dawo Abuja da bayanai saboda haka ya ga ya dace ya tura tawagarsa zuwa Abujan domin ta taimakawa shugabannin tare da sa ido.
Dangane da rade-radin cewa shugaba Barrow zai binciki Yahya Jammeh da zara ya kama madafin iko sai Fate yace sabon shugaban kasar bai taba yiwa kowa barazana ba, bai kuma taba yiwa shugaba Jammeh barazana ba. Haka bai taba gayawa kowa zai gurfanar da shugaba Jammeh gaban shari'a ba. Yace kurakuren Jammeh ba su ne damuwarsu ba. Damuwarsu ita ce yadda zasu ci da kasar gaba.
Dangane da cewa idan Yahya Jammeh yaki ya mika mulki kuma kasashen Yammacin Afirka suka ce zasu yi anfani da karfin soji su kawar dashi, sai Fate yace baya shakkan Adama Barrow zai dare kan mulki ranar 19 ga wata mai zuwa. Yace ko shakka babu Gambia zata samu sabon shugaban kasa watan gobe.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.