A kasar Nijar shugaban kungiyar muryar talaka Nasiru Seidu na ganin akwai alamar samun nasarar abun da aka sa gaba, wato shawo kan badakalar siyasa da ta kunno kai a kasar Gambia.
Yace shugaba Jammeh na tsoron abun da zai faru dashi bayan ya mika mulki wa wanda ya lashe zaben ne. Yayi tsammanin zai bada mulki kuma za'a zauna lafiya amma sai kwatsam wasu maganganu na tasowa tsakanin su wadanda suka ci zaben. Yace abun da Yahya Jammeh zai nema daga tawagar shi ne tabbaci babu abun da zai faru dashi idan ya mika mulki, za'a bar shi ya koma gonarsa ya cigaba da rayuwa.
Acewar Nasiru Seidu tunda tsoro ya kamashi ba zai yadda da sabon shugaban kasa ba Adamu Barrow dole sai an samu shaidu kamar ita tawagar da ta tafi kasar ko kuma ta Majalisar Dinkin Duniya.
Saidai shugaban kungiyar Mojan Siraji Isa ra'ayinsa ya sha banban da na Nasiru Seidu. Yace kasar Gambia ba ita ba ce ta farko inda irin wannan abu ya faru amma kuma babu abun da aka yi saboda haka bai ga rawar da tawagar zata iya takawa ba a lamarin.
Har wa yau Nasiru Seidu na ganin wannan dalilin da Siraji Isa ya bayar ba zai kawo cikas ga sakamakon zaben ba saboda duk wadanda suke cikin tawagar zabensu aka yi a kasashensu. Cikinsu ma akwai wanda aka kadashi a kasarsa wato shugaban kasar Ghana. Irin wannan misali ne da yakamata Yahya Jammeh ya bi. Ya kamata ya sani ana iya faduwa a zabe a kuma zauna lafiya.
Shugaban jam'iyyar PND Sumaila Ahmadu yana kallon sasantawar a wani karan tsaye ga dimokradiya. Yace babu batun cewa za'a lallasheshi domin idan haka za'a yi to dimokradiya kanta ta koma gurguwa. A kawar dashi ko ta halin yaya kana ya fuskanci hukumci saboda mulkin kama karya da ya yiwa mutane, inji Sumaila Ahmadu.
Ga rahoton Souley Mummuni Barma da karin bayani.