Ganin cewa shugaba Mohammadu Buhari da Yahya Jammeh baki dayansu tsoffin sojoji ne hakan yasa masu fashin baki ke muhawarar yadda wannan aikin sasantawar zai yi tasiri.
Sai dai a cewar mai magana da yawun shugaban kasa mallam Garba Shehu, an zabi shugaba Buhari a matsayinsa na dattijo kuma wanda aka zaba shugaban farar hula a Najeriya, hakan yasa aka bashi wannan amana, kuma maganar zama soja a baya bata da wani tasiri.
Masu sharshi irin su Hassan Gimba, na ganin tsohon shugaban kasa Dakta Goodluck Jonathan shi yafi cancanta ya jagoranci wannan tattaunawa ba shugaba Buhari ba. ya kara da cewa kamata yayi shugaba Buhari ya tsaya wajen sasanta matsalolin dake Najeriya.
Shi kuma kwararren jami’in diflomasiya Ambasada Yusuf Mamman, na fatan Allah ya kiyaye tabarbarewar harkokin tsaro a kasar Gambia, kasancewar ta karamar kasa. Haka kuma yayi kira ga wanda ya lashe zaben Adama Barrow, da ya san yadda zai rika furta kalamansa.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.