Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi Allah wadai da wasu sakonni da aka aikawa wasu manyan tsoffin jami’an gwamnati dauke da bam, yana mai kwatanta lamarin a matsayin abin “kyama.”
Trump wanda ya nuna “tsananin bacin ransa”, ya kara da cewa Amurka ba ta da hurumin irin wannan dabi’a, yana mai cewa bai ji dadi da aukuwar wannan lamari ba.
Sakonnin na bam an aika su ne ga tsohon shugaban kasar Barack Obama da kuma abokiyar hamayyarsa a zaben 2016 Hillary Clinton.
Har ila yau an aike da makamancin wadannan sakonni na bam ga tsohon Attorney Janar din Amurka, wanda dan majalisa ne karkashin jam’iyar Democrat da kuma tsohon Darektan hukumar leken asiri a Amurka ta CIA, wadanda duk masu yawan sukan shugaba Trump ne.
Trump ya ce za a kaddamar da wani babban bincike karkashin gwamnatin tarayya domin zakulo wadanda ke da hannu a aikawa da wadannan sakonni na bam.
“Tabbatar da lafiyar Amurkawa, shi ne muhimmin abu a gare ni.” Inji Trump
Baya ga wadannan mutane, an aikawa da ofishin yada labarai na CNN da ke birnin New York irin wannan sako mai dauke da bam.
Facebook Forum