Yau Talata Bolton zai gana da shugaban Rasha Vladimir Putin domin shaida masa dalilan da ya sa shugaba Donald Trump yake son janyewa daga yarjejeniyar kayyade makamai masu cin gajeren zango da aka samar tun alif 987.
Trump dai ya zargi kasar Rasha da karya ka’idojin yarjejeniyar.
Bolton dai yace yayi imanin cewa yarjejeniyar da aka cimma tun zamanin yakin cacar baka, yanzu haka bata da wani amfani, saboda tsarin tsaro na wannan zamanin, inda sauran kasashe ke kera makamai masu linzami.
Tsohon shugaban tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev da tsohon shugaban Amurka marigayi Ronald Reagan ne suka samar da yarjejeniyar makaman a shekakar alif 987. Wadda ta haramtawa Amurka da Rasha kera makaman ko gwajinsu.
Rasha dai ta musanta cewa ta saba ka’idojin yarjejeniyar, ta kuma ce makaman harbo makamai masu linzamin Amurka dake Turai shine ya sabawa yarjejeniyar.
Facebook Forum