Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Yi Zabe a Arewa Maso Gabas – inji Bamanga


Alhaji Bamanga Tukur.
Alhaji Bamanga Tukur.

Ganin irin tashe-tashen hankula da ake fama da su a arewacin Najeriya ne yasa Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tambayi tsohon shugaban jam’iyyar dake mulkin Najeriya PDP.

Ganin irin tashe-tashen hankula da ake fama da su a arewacin Najeriya ne yasa Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tambayi tsohon shugaban jam’iyyar dake mulkin Najeriya PDP, Alhaji Bamanga Tukur ko yana gani za’a iya gudanar da zabe a irin wannan yanayi?

“Zabe za’a yi, duk abun sulhu ne, ka san sha’anin siyasa ne”, inji Bamanga Tukur.

Bamanga Tukur ya kara da cewa “yan ta’adda, mun ga irinsu a Iraq, kuma anyi zabe, saboda haka wannan yanayi ba zai hana komai ba. Ai dole ne a sha’anin demokradiyya mu hada kai, mu yaki wannan sha’ani”.

Game da dokar ta baci kuwa a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, tsohon jagoran PDP na gani kamar babu amfani a dogara ga dokar ta baci wajen takalar ta’addanci. Yayi kira ga jama’a su tashi su yaki ‘yan ta’adda, kamar yadda Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu yayi a kwanakin baya.

Bamanga Tukur ya taba zaba shugaban jam’iyyar PDP, amma rashin fahimta tsakaninshi da wasu kusoshin jam’iyyar yasa ya aje wannan kujera, wanda yanzu ke hannun tsohon gwamnan Jihar Bauci, Ahmed Adamu Mu’azu.

XS
SM
MD
LG