Yace labarin da suka samu daga yankin Baga inda 'yan kungiyarsa suke su tare da zuwa Chadi sayen kifi ya girgizashi.
Da samun labarin sai yaje Baga daga Maiduguri domin ya ga abun da ya faru da idanunsa. Yace yadda ya ga abun da ya faru yayi bakin ciki. Abun akwai ban takaici akwai tausayawa. Duk wanda ya shiga jeji yana neman abun da zai ci aka kasheshi abun akwai bata zuciya.
Dangane da asarar rayuka da suka yi shugaban yace nan take an tsamo gawarwaki daga cikin ruwa 48 amma kuma ba iyakarsu ke nan ba domin ana cigaba da samun karin gawarwaki daga ruwan. Kana akwai wasu da ake samu jefi-jefi.
Akwai wani gari da ake kira Tungan Shanu inda 'yan Boko Haram din suka yanka mutane 24. A Tunbin Karta sun yanka mutum 5. A garin Mata sun yanka mutum 7. Akalla sun hallaka mutane 84. Yawancin mutanen da aka kashe yankasu aka yi. Wasu kuma an daure hannuwansu da kafafunsu aka jefasu ruwa.
Wasu ma da suka yi kokarin gudu an bisu an yanyankasu. Yanzu dai da wuya a cega adadin wanda da suka mutu domin bayan 84 din za'a sake samun wasu na gaba.
Ga cikakken bayani.