Wata sanarwar da jami'in labaran shugaban ya fitar Dr. Ruben Abatti ta ruwaito shugaban yana cewa akwai karin gishiri a cikin wasu rahotannin kafofin yada labarai kan tabarbarewar tsaron Najeriya.
Amma Keften Abdulmalik Yususf mai murabus daya daga cikin mazan jiya da suka fafata a yakin basasan kasar yace sun fara yaki ne da abun da aka kira "Police Action". Wato da 'yansanda suka fara yakin Biafra.
Yace yanzu ta'adancin da ake gani sai kara muni ya keyi. Su da suka yi yaki da har kunya suke ji domin yadda sojojin yanzu suke fafatawa da ta'adanci.
Yace kada shugaban kasa Jonathan ya turawa kafofin yada labarai laifi. Kafofin labarai na iyakar kokarinsu. Kullum ana karkashe mutane. Ko a Baga an kashe mutane 48. Amma shugaban ya je Landan yana zargin kafofin labaru ba daidai ba ne. Abubuwan da yakamata a yiwa sojoji ba'a yi masu ba. Ba'a basu umurnin yin aiki kamar yadda ake yi masu da.
Yace abun mamaki da zara an baiwa sojoji umurnin aiki kafin su kai wurin aikin 'yan ta'ada sun ji labari ta yaya aka yi hakan. Menene ya jawo hakan. Wannan ba komi ba ne illa sakacin gwamnati.
Bashir Mohammed Bashir wani kwararren dan jarida kuma mai sharhi kan alamuran yau da kullum yace duk adadin mutanen da aka ce sun rasa rayukansu kiyasi ne na hukuma. Rahoton dan jarida ba zai inganta sai ya ji ta bakin hukumomi da zasu tabbatar masa yadda abun ya faru. Duk lokacin da aka kai hari ko aka jefa bam idan 'yan jarida sun zo bada labari zasu ce kamar yadda hukumar 'yansanda ta shaida mutane goma ne suka rasu. Amma kuma shaidun gani da ido zasu iya cewa sun kirga gawarwaki fiye da dari.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.