Wannan na zuwa ne bayan wani kuduri da Sanata Abdullahi Danladi Sankara daga Jihar Jigawa ya gabatar a zauren Majalisar wanda ake ganin zai rage matsaloli da yawa a kasar har da ma na tsaro.
Batun yawan yara da ba sa karatu musamman a jihohin Arewa da kuma ma wadanda suka sami damar karatu amma kuma ba su da ayyukan yi kuma ba su koyi sana'a ba, shi ne ya dauki hankalin Sanata Abdullahi Danladi Sankara wanda ya koka akan cewa ire iren wadannan matasan ke yawon barace barace, kuma irinsu ne ke zama wadanda ake amfani da su wajen mugayen dabi'u da ma ta'addanci, lamarin da a yanzu ya jefa kasar a cikin yanayin rashin tsaro.
A lokacin da ya ke ganawa da Muryar Amurka a Majalisar kasa, Sanata Abdullahi Danladi Sankara ya ce Majalisa za ta ba bangaren gwamnati goyon baya wajen cimma wanan buri tunda su ne masu sa ido akan ayyukan da ake yiwa al'umma.
A na shi bayanin, Sanata Uba Sani, Mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya ya ce irin wannan matakin zai taimaka wajen farfado da masana'antu domin matasa su sami ayyukan yi, ya kara da cewa kwamitinsa na goyon bayan ba matasa kananan basussuka domin a inganta sana'o'in hannu, musamman noma saboda a sami abinci isasshe.
Shi ma Sanata Mohammed Adamu Aliero, daga Jihar Kebbi ya goyi bayan matakan kawo ci gaba a kasa wajen inganta masana'antu domin matasa su iya dogaro da kansu. Ya kuma ce idan su ka himmatu da yin amfani da abubuwan da su ka koyo a makarantunsu, hakan na iya kawo ci gaba cikin gaggawa tare da rage zaman banza da kuma yawon bara wanda ba almajirai kadai ke yi ba.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum