Babbar kungiyar 'yan hmayyan ta zargi gwamnatin Syria da laifin karin fadace fadace da suke aukuwa tun bayan da asassan biyu suka sanya hanu kan yarjejeniyar tsagaita wuta.
A wani taro da manema labarai jiya Talata a birnin Geneva, shugaban 'yan hamayya Riyad Hijab, yayi kira ga kasashen duniya a zaman magoya bayan Syria su sa baki.
Ahalinda ake ciki, 'yan gwagwarmaya a Syria sun ce wasu farmaki dajiragen yaki da aka kai kan garurwa biyu dake hanun 'yan hamayya a arewa maso yammacin Syria, ya kashe mutane 44.
Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Bil'Adama a Syria, tace farmaki da aka kai kasuwar kayan gwari, a garin da ake kira Maarat-al-Numan, jiya Talata ya kashe kimanin mutane 40. Kungiyar mai zaman kanta tace wani harin kuma da aka kai kan wani gari mai suna Kafranbel a lardin Idlib ya kashe akalla mutane hudu. An san duka yankunansuna zaman tungayen 'yan hamayya ne.