Yawan sace masu shanu da barayin keyi ya jefa al'ummar Fulani a jihar Neja cikin wani tashin hankali.
Ardo Adamu Kaduna shugaban Miyetti Allah reshen jihar Neja yace sace sacen shanu da kashe mutanensu ya addabesu a jihar Neja inda yace kawo yanzu an kashe masu mutane fiye da takwas. Baicin kashesu an yi awon gaba da dukiyoyinsu. Ardo Adamu na ganin Fulani ne da suka fito daga arewa suke aika-aikar.
Kungiyar Miyetti Allah ta kafa wata kungiyar 'yan sa kai na matasan Fulani domin tunkarar barayin kuma tuni matasan suka shiga farautar barayin shanun.
Biyo bayan kokarin matasan yanzu sun samu cafke wasu mutane ukku da ake zargin suna cikin barayin shanun tare da shanu dari daya da biyar da dimbin tumaki.
Abubakar Dikko Shakallo shugaban kungiyar matasan da Fulnin suka kafa yace sun kamo shanu a wani gari Pango inda suka samu mutane guda hudu. Daya yana rike da bindiga kirar AK47 amma shi mai bindigar ya gudu. Matasan sun kama sauran mutanen da shanun da yanzu sun kaisu Kagara wurin 'yansanda. Barayin da suka shiga hannu sun kira barawon da ya gudu kuma yayi alkawarin kawo bindigar.
Shanun suna hannun karamar hukumar Rafi inda shugaban hukumar Tanko Gambo Kagara yace ya kafa kwamitin maida shanun ga masu su.
Kakakin rundunar 'yansandan jihar DSP Bala Elkana yace suna kokarin fatattakar barayin daga jihar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.