Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa nan gaba kadan zata fito da wani tsari na samar da aikin yi ta bangaren wasanni baya ga aikin da zata bayar na mallaman makaranta da malaman gona da kiwon lafiya.
Ministan Matasa da wasanni na Najeriya Barista Solomon Dalung, yace akwai hanyoyin samar da aiki da yawa a bangaren wasanni, wadda kuma ta zamanto hanya mafi sauki wajen samarwa da matasa aikin yi. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati zata bunkasa harkar wasanni.
A karkashin shirin dai za a rika biyan wadannan matasa albashi yayin da suke aikin koyarwa kafin su samu aiki.
Wannan shiri dai daya ne daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin Najeriyar ta yi alkawarin aiwatarwa don inganta rayuwar al'ummar kasar.
Domin karin bayani.