bayyana damuwa kan yadda za a tunkari nasarorin da suke samu na kula da mutanen da ake ci gaba da kamawa.
An tuhumi wadansu karin mutane biyu da ake kira Smail F da Ibrahim F da laifin ta’addanci da kisan kai dangane da hare haren da aka kai a Brussels da suka yi sanadin mutuwar mutane 32. Masu shigar da kara na kasar Belgium sun sanar a kafofin sadarwar kasar cewa, mutane biyun wa da kani ne.
‘Yan sandan Brussels sun kuma tsare wadansu mutane uku bayan gudanar da bincike a gidajensu dake babban birnin lardin Uccle.
Ba a yi wani karin haske dangane da tsare mutanen ba, sai dai kafofin sadarwar kasar Kenya sun yayata cewa, alkali zai yanke hukumci yau Laraba kan ko za a ci gaba da tsare mutanen uku.