Mai gabatar da kara na kasar Belgium yace sun sallami mutane 3 daga cikin wadanda suka kame ranar talata domin binciken harin da aka kai a kasar Paris a ranar 13 ga watan nuwamba wanda yayi dalilin mutuwar mutane 130
Ofishin mai gabatar dakarar ya fada yau laraba cewa ba daya daga cikin mutanen da aka gurfanar, sai dai kawai an tsare su ne ranar talata lokacin da ‘yan sane ke bincike a gundumar Brussel, lokacin da jamiaan Belgium ke kokarin kame wadanda suka kai harin Paris da kuma na tashan jirgin saman Brussel wanda yayi dalilin mutuwar mutane 32 a cikin watan da ya gabata.
A ranar talata mutane biyu da aka bayyana sunayen da Smail F. da Ibrahim F.an kama su kuma an tuhume su da hanu wajen kai harin da aka kai cikin watan jiya a Brussel.
Mai gabatar da kara na kasar ta Belgium ya bayyanawa kafofin yada labarai na cikin gida cewa wadannan mutanen biyu da aka kama ‘yan uwan juna.
Sai dai kasar ta Belgium ta sha suka akan nuna sakaci akan tattara bayanan sirri da kuma daukan matakan tsaro kan kari akan wannan harin na Brussel da na Paris, musammam ma yadda ya dauke ta har tsawo watanni hudu kafin ta kame jigo a harin Paris wato Salah Abdesalam.
Sai kuma ‘Yan sandan kasar Belgiuum sunyi kame-kame kafin da kuma bayan harin na Brussel.