Saboda haka magoya bayan shugaban suka hallara a filin kwallon kafa da ake kira Huseni Kounche domin cashewa da rawa a kade kade.
Daga bisani shugaban mai neman wa'adi na biyu a fafatawar da zai yi da 'yan takara kimanin 14 ya kara jaddada burin lashe zaben da za'a yi ranar 21 ga wannan watan a zagayen farko.
Shugaban yana buga kirji ne ayykan da yace ya yi cikin shekaru biyar din da suka gabata. Yana kuma dogaro da goyon bayan da yace ya samu daga jam'iyyu guda 40.
Amma babbar jam'iyyar adawa MNSD Nasara wadda dan takaranta ke rufe nashi gangamin a Maradi na cewa zuwa zagaye na biyu a wannan zaben babu makawa, wato dole ne a je zagaye na biyu. Tambura Issoufou sakataren watsa labaran jam'iyyar yace duk wadanda suka taru a Niamey wurin gangamin PNDS magoya bayan MNSD ne. Karya PNDS ke yi. Kudi suka ba mutane su taru.
Duk abun da shugaban yace zai yi bai yi ba. Wadanda bai ce zai yi ba ya yi. Hanyoyin ma da ya yi ya zabga kudi fiye da kimani domin sata. Aikin miliyan biyu sun ce sun kashe miliyan 17.
Ga karin bayani.