A daidai lokacin da aski ya kawo gaban goshi a zaben gama gari da za'a yi a jamhuriyar Nijar manyan 'yan siyasa sun soma maganganun dake karo da juna tsakanin dan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya dake samun goyon bayan jam'iyyu arba'in da na MNSD Nasara.
Alhaji Mahamadou Issoufou na PNDS da abokin hamayyarsa na MNSD Seni Umar madugun 'yan adawa da tsohon shugaban kasa Muhamadou Tanja su ne suke caccakar juna.
Maganganun nada nasaba ne da yadda kowannensu ke ganin yadda zaben ranar 21 ga wannan watan zai kaya.
Shi dai shugaba mai ci yanzu Mahamadou Issoufou ya sha alwashin lashe zaben a karon farko ba sai an yi zagye na biyu ba kamar yadda aka saba. Yaba bada hujjoji uku da zasu sa hakan ya faru.
Na farko yace yana da goyon bayan jam'iyyu 43. Abu na biyu shi ne ayyukan da ya yi cikin shekaru biyar da suka gabata. Dalili na uku kuwa shi ne ayyukan da ya tsara zai yi a shekaru biyar masu zuwa. Yace su 'yan kasa da kansu suka ce zaben shugaban kasa a wannan karon ba zai ci lokaci ba. Karon farko zasu tsayar da shugaba.
Amma Alhaji Seni Umar madugun 'yan adawa yace ba zata yiwu a samu shugaban kasa a karon farko ba.Amma su ne zasu karbe mulki bayan zaben.
Ga karin bayani