A shekarar 2008 Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan rana bayan harin da aka kai akan hedkwatarta da ke Bagadaza a Iraqi a shekarar 2003.
Akalla ma’aikatanta 22 ne suka rasa rayukansu har da shugabansu Sergio Vierra de Mello.
Tun kuma daga wannan lokacin ne, ake ci gaba da kai hare-hare akan ma’aikatan jin kai yayin da su ke ba da agajin gaggawa.
Wani rahoto da Hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, ta fitar ya nuna cewa ce an kashe ma’aikatanta 603 kana an jikkata wasu 958 a hare-hare 32 da aka kai a kasashe 2014.
Baya ga haka bayanai na nuni da cewa kasashe irinsu Syria da Yamal da Afghanistan da ke fama da rikice-rikice, na daga cikin kasashen da aka fi kai hare-hare akan ma’aikatan jin kai.
Kuma ma'aikatan Kungiyar likitoci ta kasa da kasa, wato Doctors Without border, suna daga cikin wadanda aka fi kai hari a kansu, musamman a Syria da Yamal.