A wata tattaunawa da wakilin Muryar Amurka, Chief Usaini Abubakar sarkin Yamman Keffi kuma Galadiman Akinyele Ibadan, yace babban abinda yakamata gwamnatin tarayya tayi yanzu shine ta san inda aka ajiye ‘yan matan Chibok, idan har sai an nemi taikamakon Turawan kasashen waje ne domin su yi amfani da na’urorin zamani don gano inda su ke.
Haka kuma basaraken ya shawarci gwamnatin tarayya da ta yi hattara wajen sakar ‘yan kungiyar dake hannunta domin kungiyar ta bayar da ‘yan matan. A kuma bincika cikin ‘yan Boko Haram din da ke hannun gwamnati, a duba wadanda laifinsu bai taka kara ya karya ba a sake su domin su ma su saki ‘yan matan.
Kan batun yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Sarki Usaini, yace matsalar wannan gwamnatin shine kan rashin yiwa ‘yan Najeriya bayanin halin da ake ciki game da mutanen da ka cafke da laifin sace kudaden ‘kasa.
Saurari cikakkiyar hira da Chief Usaini.