Ana kara karfafa zaton cewa da kyar za’a samu wata gagarumar nasara a ganawar da ake shirin yi tsakanin Shugaban Palastine Mahmoud Abbas da Shugaban Amurka Donald Trump a yau Laraba a White House.
Satin da ya gabata Trump yace “bai ga dalilin da za a ce zaman lafiya bai yiwuwa tsakanin Israila da Falasdinu. Haka kuma Abbas zai yiyuwa a cimma yarjajeniyar tarihi da zata kawo karshen rikicin da aka kwashe sama da shekaru 10 ana yi, sakamakon shiga tsakani da shugaba Trump ke yi.
Abbas wanda yake jagorantar Hukumar Falasdinu dake yammacin Kogin jodan bai da buri mai yawa dangane da ribar zuwan nashi Washington. A cewar jami’an Falasdinu, daya daga cikin bukatunsa shine ya ji shirin Trump na farfado da ganawar samar da zaman lafiya a yankin.
Amma masu fashin baki sun ce, Abbas na fatan tattaunawar zata farfado masa da martabarsa da ta dakushe a gida da kuma waje.
Facebook Forum