Tururuwar mutane ne suka hallara a mashigar garin Yamai domin tarbar shugabannin kungiyoyin fararen hula da kotu ta sallama, bayan sun shafe watanni 4 a gidan yari, saboda zargin shirya zanga-zanga ba da izinin hukuma ba.
Shugaban kungiyar ROTAB Ali Idrissa, da ke daya daga cikin ‘yan fafutukar da aka tsare a gidan kaso saboda dalilai masu nasaba da adawa da dokar harajin 2018, ya bayyanawa manema labarai cewa suna nan akan bakarsu. A cewarsa, yanzu ma suka fara gwagwarmaya.
Za dai a ci gaba da tsare wasu mutane 6 daga cikin wadanda aka kama a ranar 25 ga watan Maris domin zaman kurkuku na watanni 6, yayin da wasu ‘yan gwagwarmayar da aka kama a Zinder, da wasu da ke a rukuni na biyu na ‘yan gwagwarmyar da aka kama a ranar 15 Afrilu a Yamai, ake jiran jin yadda makomarsu za ta kasance.To amma Gamatche Mahamadou na cewa sai sun daukaka kara saboda ba su yarda cewa sun aikata laifi ba.
Tun a ranakun farko na zanga-zangar ne ma’aikatar magajin garin Yamai ta bukaci kotu ta ci tarar ‘yan fafutukan makudan kudade a matsayin diyya, sai dai rashin gabatar da hujjoji ya sa alkali yin watsi da wannan bukata, matakin da masanin dokokin tsarin mulki Dakta Bubakar Amadu Hassan ke ganin za a iya dogara da shi don zuwa kotu ta gaba.
Tuni dai Nouhou Arzika, da Moussa Tchangari da wasu daga cikin wadanda kotu ta sallama suka koma gidajensu. Yayin da Lirwana Abdourahmane wani lauyan mai zaman kansa ke fara zaman kurkuku na tsawon shekara guda, bayan da ya kasa gabatarwa kotu hujjar da ke gaskanta zargin cin hancin da ya ce wani alkali ya karba domin ya rufesu a gidan kaso.
Saurari rohoton
Facebook Forum