Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Kotu Ta Sallami 'Yan Fafutukar Adawa Da Dokar Harajin 2018


Lauya Me Boudal Effred da tawagar lauyoyin dake kare jami'an fafitika
Lauya Me Boudal Effred da tawagar lauyoyin dake kare jami'an fafitika

Kotun birnin Nyamai ta umurci hukumomin jamhuriyar nijer su sallami jami’an fafitikar da suka garkame a gidajen yarin yankin Tilabery tun a ranar 25 ga watan Maris saboda zarginsu da gudanar da zanga zanga ba da izinin hukuma ba

Hukumi na zargin jami’an fafitikar kungiyoyin CCAC da yunkurin tayarda zaune tsaye tare da farfasa dukiyoyin jama’a a yayin haramtaciyar zanga zanga a ranar 25 ga watan maris dalili kenan da hukumomin nijer suka bukaci kotu ta masu daurin shekara ukku ukku a gidan yari sai dai bayan nazari akan hujojin da bangarori suka gabatar alkali ya sallami wadanan ‘yan farar hula Me Boudal Effred yana daga cikin lauyoyin dake kare wadanda ake tuhuma, yace kotu ta goyi bayan biyu da ga cikin bukatoci uku da suka gabatar…

Tururuwar ‘yan uwa da aminnan arzikin da suka halarci kotun a dazu da hantsi sun nuna farin cikin akan wannan hukunci…

Sai dai wasu daga cikin mutane sama da 20 din da aka garkame a gidajen kason yankin saboda zanga zangar ta watan maris zasu ci gaba da zama a tsare saboda samunsu da hannu dumu dumu wajen tayarda tarzoma abinda hukuncin da lauyoyi suka kudiri anniyar kalobalanta a take..

Ya zuwa yanzu lauyoyin gwamnati ba su bayyana matsayinsu akan hukuncin kotun ba kamar yadda a bangaren hukumomi ba wani jami’in da ya yi tsokaci game da matakin sakin wadanan mutane da shugaban kasar nijer Isuhu Mahammadu a can baya ya zarga da yunkurin kifarda gwamnatinsa ta hanyar shirya zanga zangar tsakar dare.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma

Kotu Ta Sallami 'Yan Fafutuka a nijar-4"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG