‘Yan sandan Faransa sun cafke wani mutum mai shekaru 29 a birnin Paris, yayin da ake ci gaba da kai samame a duk fadin kasar, domin zakulo wadanda suka kai harin da kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaiwa a watan da ya gabata.
Ya zuwa yanzu ‘yan sandan Faransa sun kaddamar da samame dubu biyu da dari bakwai, tun bayan harin na Paris da ya kashe mutane 130, lamarin da ya ba da damar aka yiwa mutane 360 daurin talala.
Ofishin mai shigar da kara a birnin Paris ya kuma ce ‘yan sanda sun tsare wani mutum da mata a arewacin Faransa, bayan da aka zargesu da taimakawa wani mutum da ya kai hari a shagon sayar da kaya na Kosher a watan Janairu.
Cafke mutanen da aka yi na zuwa ne kusan shekara guda bayan da aka kai harin gidan jaridar Charlie Ebdo da kuma wanda aka kai a shagon sai da kayan, inda jumullar mutane 17 suka mutu.
Yanzu haka ana neman wani mutum mai shekaru 26 dan asalin kasar Faransa, wanda ‘yan sanda suka yi amannar cewa ya taka rawa a harin Paris, wanda kuma yanzu haka aka fitar da takardar izinin cafke shi a duk kasar da aka ganshi.