Minista Chaudhry Nisar Ali Khan, ya fadi hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai, inda ya bayyana abinda hukumomin Pakistan suka sani game da Tashfeen Malik mai shekaru 29.
Khan ya kara da cewa iyayen matar sun zauna a Saudi Arabia har na tsawon shekaru 25, inda a nan ne ‘yan uwanta maza da mata suka girma.
A cewarsa, ta kuma halarci jami’ar Pakistan, amma kuma babu wata hujja da ta nuna akwai alaka tsakaninta da mayakan Islaman kasar.
Khan ya kara da cewa, Pakistan ta baiwa Amurka goyon baya ta fuskar shari’a wanda abu ne da ya rataya a wuyanta.
Har ya zuwa yanzu, hukumomi a Amurka na kokarin gano dalilin da ya sa Malik da mijinta Syed Rizwan Farook, wanda haifaffan Amurka ne, suka kashe mutane 14 tare da raunata wasu 21 a wani wajen taro da aka shiryawa ma’aikatan karamar hukumar San Bernadino da ke California.