Wannan doka dai ta maida hankali ne kan tsarin kyale marasa visa daga kasashe 38 da Amurka ta amince da su, su shiga kasar ba tare da karbar visar ba daga wani ofishin jakadancin Amurka, inda za a barsu su zauna har na tsawon kwanaki 90 ko kasa da haka.
‘Yan majalisu 407 suka amince da kudirin dokar yayin da 19 kacal suka nuna adawarsu a zaman majalisar da aka yi a jiya Talata.
Dokar har ila yau za ta samar da sauyi kan irin visar da za a baiwa wadanda suka fito daga kasashen Iraqi da Syria, da sauran kasashen da ake musu kallon tungar ‘yan ta’adda ne, da kuma duk wanda ya kai ziyara wadannan kasashe cikin shekaru biyar da suka gabata.
Wannan matsaya da Majalisar wakilan ta cimma, za ta bukaci kasashen da ke cin gajiyar shirin shiga Amurka ba tare da visa ba, su yi binciken kwakwaf akan matafiya daga kasashen, domin a tabbatar basa cikin wadanda ake nema ruwa a jallo bisa dalilai da suka shafi ayyukan ta’addanci.
Akalla mutane miliyan 20 ke kawo ziyara nan Amurka a duk shekara a karkashin wannan shirin, wadanda akan tantance su kafin su shiga kasar ba tare da visa ba.