Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanayi Na Kara Dagula Kokarin Kashe Gobarar Daji A Jihar California


Wata mota na shigewa kan hanya a yayin ad wutar daji ke kona gefen wani dutse a kudu da garin Casitas Springs, California
Wata mota na shigewa kan hanya a yayin ad wutar daji ke kona gefen wani dutse a kudu da garin Casitas Springs, California

Magajin Garin Los Angeles, Eric Garcetti ya ce ya zuwa yanzu, an kwashe sama da mutane dubu 230 a tsakanin Birnin da karamar hukumar da ake kira Ventura.

Hukumomi a kudancin jihar California sun yi gargadi kan aukuwar wani matsanancin yanayi a yau Alhamis, inda suka ce za a samu bushasshiyar iska mai kadawa, wanda hakan zai kara dagula al’amura a kokarin da ake yi na shawo kan guborar dajin da ta barke a makon nan a Birnin Los Angeles.

“Bari na fada muku karara, ba mu da kayayyakin da za su taimaka mana wajen dakile wannan yanayi da aka yi hasashe,” inji Darektan hukumar kashe gobara a jihar California, Ken Pimlott.

A daren yau Alhamis ake sa ran iskar mai tafiyar kilomita 120 cikin sa’a guda, za ta fara kadawa, lamarin da ya sa shugabannin hukumar kashe gobarar suka ba da gargadin cewa kowa ya kwanta da idonsa daya a bude.

Sannan an gargadi al’umar yankin da su arce daga gidajensu da zaran sun ga wata alama mai cike da barazana.

A wani sakon Twitter da ya aike, shugaba Trump ya yi kira ga mazauna yankunan da su karbi shawarawarin da aka basu na ficewa daga yankunan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG