Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Tayi Tur Da Kisan Musulmi A Myanmar


'Yan gudun hijirar Rohingya da suka tsallake kogin Naf
'Yan gudun hijirar Rohingya da suka tsallake kogin Naf

Majalisar wakilan Amurka ta yi Allah wadarai da matakan kashewa da korar 'yan kabilar Rohingya, inda ta zartas da kudurin da yayi kiran da a kawo karshen farmakin da ake kaiwa kan wadannan Musulmi 'yan tsiraru a kasar ta Myanmar ko Burma.

Kashi biyu cikin uku na 'yan majalisar suka amince da wannan kudurin.

Wannan kudurin shine matakin farko a irin matakan da majalisar zata iya dauka, wadanda zasu iya hadawa da takunkumi na matsin lambar kudi kan sojojin Burma, tare da bayar da gudumawar tattalin arziki na Amurka domin sake mayarwa da kuma tsugunar da 'yan Rohingya wadanda a yanzu suka gudu zuwa kasar Bangladesh.

Shugaban kwamitin hulda da kasashen waje na majalisar, Ed Royce, dan jam'iyyar Republican daga Jihar California, yace "wannan batu ne na imani, kuma na tsaron kasa. Babu wanda zai zauna cikin kwanciyar hankali idan har aka ci gaba da shuka tsageranci da zaman dar-dar a wannan bangare na duniya."

An kori 'yan kabilar Rohingya da aka kiyasta sun kai dubu 600 daga gidajensu cikin 'yan watannin nan, inda suka gudu zuwa Bangladesh tare da janyo babbar matsalar jinkai.

Royce yace, "An kashe daruruwan mutane, an kona kauyuka akalla 200 kurmus, an kuma dasa nakiyoyi a bakin iyakar Burma da Bangladesh suna kashewa da nakkasa 'yan gudun hijirar dake neman mafaka. Akwai rahotannin fyade da farmaki nau'i-nau'i kan 'yan Rohingya."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG