Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce Amurka da kawayen ta na kungiyar tsaro ta NATO na duba yiwuwar yin amfani da hanyoyi da dama, a ciki yin amfani da sojoji wajen dakatar da abun da ya kira al’amarin da ba za a yarda da shi ba, wato jidalin da gwamnatin Libiya da magoya bayan ta ke yiwa masu neman canji.
A yau litinin shugaba Obama ya fada a fadar shi ta White House cewa so yake yi ya aike da bayyanannen sako zuwa ga mutanen da ke yiwa shugaban Libiya Muammar Ghaddafi aiki, cewa za a hukunta su akan zabin da su yiwa kan su.
Haka kuma Shugaba ya ce ya bada izini a kara dola miliyan 15 a kan kudaden agazawa al’ummar kasar Libiya.
Shugaban ya yi wannan furuci ne bayan ya gama tattaunawa dad a frayim ministar kasar Australia Julia Gillard. Ya ce ra’ayin Amurka da na Australia ya zo daya a kan kasar Libiya, wannan ra’ayi kuwa shi ne dagewa wajen tabbatar da demokradiya a inda ake jefa jama’a cikin tashin hankali babu hujja.
Mr. Obama ya godewa sojojin kasar Australia saboda gagarumar gudunmawar da su ke bayarwa a kasar Afghanistan. Kuma ya yi ta’aziyar wadanda ambaliyar ruwa ta halaka a jahar Queensland a kasar Australia a cikin watan janairu.
Watch video of the events in Libya