Tawagar ‘yan wasan kasar Senegal “The Lions of Teranga” sun isa Kamaru don shirin fara karawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON.
A ranar 9 ga watan Janairu za a fara gasar. Senegal za ta fara karawa ne da kasar Zimbabwe a ranar Litinin.
Dan wasan Liverpool Sadio Mane da mai tsaron ragar Chelsea Edouard Mendy na daga cikin taurarin ‘yan wasa a tawagar ta Senegal.
“The Lions of Senegal sun isa Kamaru.” Hukumar kwallon kafar kasar ta Senegal ta wallafa a shafinta na Facebook.
Gabanin kungiyar ta taso daga Dakar, babban birnin na Senegal, an dan samu jinkiri bayan da aka gano wasu 'yan wasa uku da wasu 'yan tawagar tafiyar sun kamu da cutar COVID-19.
Hukumar kwallon kafa ta Senegal ta bayyana sunayen ‘yan wasan a ranar Laraba a matsayin Pape Sarr, Nampalys Mendy da kuma Mame Thiam.
Senegal ita ce ta zo ta biyu a wasan karshe da ta buga da Aljeriya a gasar ta AFCON ta shekarar 2019. Aljeriya ta doke Senegal da ci 1- 0 ta lashe kofin.