Kungiyar ‘yan wasan Najeriya Super Eagles ta bayyana dalilin da ya sa ba a kira dan wasan Leicester City Ademola Lookman ba a cikin tawagar ‘yan wasan na Najeriya.
A makon da ya gabata kungiyar ta fitar da jerin ‘yan wasa 28 da za su wakilce ta a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON da za a fara wannan wata a Kamaru.
Sai dai babu sunan Lookman a cikin, wanda dan wasan Leicester City ne a gasar Premier League ta Ingila, lamarin da ya janyo suka daga wasu ‘yan Najeriya.
Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar a karshen makon da ya gabata, Super Eagles ta ce har yanzu hukumar kwallon kafa ta FIFA ba ta kammala tantance dan wasan ba.
“Har yanzu FIFA ba ta kammala tantance Ademola Lookman ba don ya wakilci Najeriya a matakin aksa da kasa, ana kan bin matakin da dan wasan zai iya bugawa Najeriya.” In ji sanarwar.
“Saboda kuskure ne wata kafa ta ce mai horar da ‘yan wasa na wucin gadi Augustine Eguavoen ne ya cire shi daga jerin ‘yan wasan Najeriya 28 da za su je AFCON a Kamaru.”
A cewar sanarwar, an saka sunan Lookman a jerin ‘yan wasan a mataki na farko, bisa tunanin cewa za a kammala tantance shi kafin a fara gasar ta AFCON.
Lookman shi ya ci Liverpool kwallo da ta ba Leicester City nasara a karawar da suka yi a ranar Talatar da ta gabata.