Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ba Kungiyoyin Turai Damar Rike ‘Yan wasan Afirka Har Zuwa Makon Farko Da Za A Fara Gasar AFCON


'Yan wasan Liverpool Sadio Mane, hagu da Mohamed Salah, dama
'Yan wasan Liverpool Sadio Mane, hagu da Mohamed Salah, dama

Za dai a fara gasar cin kofin nahiyar ta Afirka da kasashe 24 a ranar 9 ga watan Janairu a birnin Yaounde da ke Kamaru.

An ba kungiyoyin kwallon kafar nahiyar turai damar jinkirta sakin ‘yan wasansu da za su kara a gasar cin kofin nahiyar Afirka har zuwa makon da za a fara gasar.

Ka’idojin FIFA sun nuna cewa, wajibi ne a saki ‘yan wasan su koma kasashensu na asali a Afirka nan da wannan ranar Litinin da aka shata.

Amma yanzu kungiyoyi za su iya rike ‘yan wasan har sai ranar 3 ga watan Janairu kafin su sake su.

Za dai a fara gasar cin kofin nahiyar ta Afirka da kasashe 24 a ranar 9 ga watan Janairu a birnin Yaounde da ke Kamaru.

Za kuma a kammala gasar da wasan karshe a ranar 6 ga watan Fabrairu.

Mataimakin Sakatare Janar na kungiyar kwallon kafa ta FIFA Mattias Grafstrom ne ya rubutawa hukumar wasika a ranar Asabar da hukumomin gasa da ake bugawa a turai dauke da wannan sauyi da aka yi, wasikar da kamfanin dillancin labarai ta AP ta ce ta gani.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG